NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa Ake Hana ’Yan Najeriya Fadin Albarkacin Bakinsu

Shirin Najeriya A Yau zai yi duba a kan tanade-tanaden doka a kan ’yancin faɗin albarkacin baki a Nijeriya. Shin me ya sa ake hana ’yan ƙasar faɗin albarkacin bakinsu?

NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa Ake Hana ’Yan Najeriya Fadin Albarkacin Bakinsu

Wasu matasan Najeriya a lokacin wata zanga-zanga a kan titin Legas-Ibasan kan cin zalinsu da ‘yan sanda ke yi. (Hoto:PIUS UTOMI EKPEI / AFP) (Photo by PIUS UTOMI EKPEI/AFP via Getty Images)

Sashe na 4 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na ɗauke da tanade-tanade musamman da suka shafi ’yancin ɗan Adam a dokar Najeriya.

Cikin tanade-tanaden akwai ’yancin da doka ta bai wa kowane ɗan Nijeriya na rayuwa da shiga taro da kuma faɗin albarkacin baki.

Shirin Najeriya A Yau zai yi duba a kan tanade-tanaden doka a kan ’yancin faɗin albarkacin baki.

Domin sauke shirin, latsa nan