NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa Ba Mu Bayar da ‘Ramadan Basket’ Ba

A bana abin ya sauya salo, domin kuwa ba kamar yadda aka saba ba, kafafen sada zumunta ba su baza hotuna da bidiyon Ramadan Basket ɗin ba.

NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa Ba Mu Bayar da ‘Ramadan Basket’ Ba

A al’adance, a duk lokacin da watan Ramadana ya ƙarato samari da ’yan mata kan yi musayar kyaututtuka domin kyautata wa juna.

Misali, samari kan haɗa kayan buɗe-baki irinsu madara da ƙwai da sauran kayan maƙulashe da ake yi wa lakabi da ‘Ramadan Basket’ a turance su kai wa ’yan matansu.

Sai dai a wannan shekarar da alamun abin ya sauya salo, domin kuwa ba kamar yadda aka saba ba, kafafen sada zumunta ba su baza hotuna da bidiyon Ramadan Basket ɗin ba.

Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi duba ne kan dalilan da suka hana samari yin ‘Ramadan Basket’ wannan shekarar.

Domin sauke shirin, latsa nan