NAJERIYA A YAU: Shin Ganawar Atiku Da Obi Na Kaɗa Hantar APC?

Jam’iyar APC ta bukaci ‘yan Najeriya kada su aminta da Atiku da Obi.

NAJERIYA A YAU: Shin Ganawar Atiku Da Obi Na Kaɗa Hantar APC?

Alƙiblar siyasa da ke kaɗawa daga ɓangaren ’yan adawa ta fara daukar hankalin jam’iyya mai mulki a Najeriya.

Yawaitar ganawar da wasu jiga-jigan adawa na yi ta sa ana neman sanin me ke shirin faruwa, lamarin da jam’iuyar APC ta ce ’yan Najeriya za su bude idanunsu kada su yarda da irin mutanen da ta ce suna kasuwar bukata.

Toh shin wannan ganawa na rikita APC ne?

Shirin Najeriya a Yau ya yi nazari kan yadda ganawar jam’iyyun adawa ta fara kaɗa guguwar siyasar kasar.

Domin sauke cikakken shirin, latsa nan