NAJERIYA A YAU: Dalilin Watsi Da Dokar Ba Mata 35% na mukaman shugabanci

Dalilan watsi da dokokin kebe wa mata mukaman shugabanci da sauransu.

NAJERIYA A YAU: Dalilin Watsi Da Dokar Ba Mata 35% na mukaman shugabanci

Domin sauke shirin latsa nan

Mata a Najeriya na ci gaba da kumfar baki bayan majalisar dokokin kasar ta yi fatali da kudurin dokar wajabta ware musu kashi 35 cikin 100 na mukaman gwamnati da na jam’iyyun siyasa.

Matan suna kuma bukatar majalisa ta kafa doka cewa duk mijin da suka aura dan wata kasa to ya zama dan Najeriya, albarkacinsu.

Shirin Najeriya A Yau na dauke da dalilan da suka sa kudurorin dokar ba su kai labari ba.