NAJERIYA A YAU: Ainihin Dalilan Taƙaddama Kan Kafa Kotunan Musulunci A Kudu

Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci a yankin ce dai ta buƙaci hakan. Sai dai wasu ƙungiyoyi da ma ɗaiɗaikun mutane a yankin suna adawa da wannan buƙata.

Wata kotun shari’ar Musulunci (Tsohuwar ajiya)

Ana ci gaba da zazzafar muhawara a shiyyar Kudu maso Yammacin Najeriya a kan batun samar da kotunan Shari’ar Musulunci.

Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci a yankin ce dai ta buƙaci hakan. Sai dai wasu ƙungiyoyi da ma ɗaiɗaikun mutane a yankin suna adawa da wannan buƙata.

Wannan ne batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lokacin zai yi nazari a kai.

Domin sauke shirin, latsa nan