NAJERIYA A YAU: Alfanu Da Kalubalen Sabon Jadawalin Karatun Makarantu Da Gwamnati Ta Bijiro Dashi
Wadanne irin alfanu ko kalubale sabon tsarin jadawalin karatun firamare da sakandare zai fuskanta yayin da gwamnati ta bijiro dashi?
A kwanakin baya, Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da sabon tsarin jadawalin karatu ga makarantun firamare da sakandare. Sabon tsarin, wanda Ma’aikatar Ilimi ta ƙasa ta tsara, yana da nufin inganta koyarwa da koyo, da rage nauyin lodi ga dalibai, da kuma tabbatar da cewa malamai suna da isasshen lokaci don isar da darussa tare da kwarewa.
Tsarin ya mayar da hankali kan daidaita ranakun makaranta, da tsara lokutan darussa bisa bukatun shekaru da matakin karatu, da kuma kara aiki a kan basira, da kirkire-kirkire, da koyon sana’o’i, domin shirya dalibai su zama masu amfani a harkokin tattalin arziki tun daga matakin makaranta.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Abincin Da Mutane Ke Ci Ke Zamewa Guba
- DAGA LARABA: Ko Ziyarar Tawagar Amurka Za Ta Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya?
Shin ko wadanne alfanu ko akasin haka wannan canji zai haifar a fannin ilimi a kasar nan?
Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan