NAJERIYA A YAU: Barkewar Cutar Kyanda: Sakaci Ko Annoba?

Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi gargadin cewa cutar kyanda na ci gaba da zama barazana ga yara a Najeriya.

NAJERIYA A YAU: Barkewar Cutar Kyanda: Sakaci Ko Annoba?

A karshen shekarar 2023 Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da Cibiyar Hana Yaduwar Cututtuka ta Ƙasa (NCDC) suka yi gargadi cewa cutar kyanda na ci gaba da zama barazana ga yara a Najeriya.

A baya-bayan nan kuma sai ga shi an samu rahotan barkewar cutar a wasu yankunan kasar har ta kashe mutane da dama.

Shirin Najeriya a Yau ya mayar da hankali ne kan cutar ta kyanda da kuma yadda za ku kare yaranku daga gareta.

Domin sauke cikakken shirin, latsa nan

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta