NAJERIYA A YAU: Ce-ce Ku-ce Da Ya Dabaibaye Dauke Shalkwatar Bankin Masana’antu Zuwa Legas
Irin takaddamar da ta kaure tsakanin wadanda ke goyon bayan dauke shalkwatar bankin masana’antu da wadanda ke ganin hakan na da wata illa.
Batun matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na mayar da shalkwatar Bankin Masana’antu zuwa jihar Legas ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin ’yan Najeriya. Wannan mataki ya tayar da mabanbantan ra’ayoyi daga bangarori daban-daban na al’umma, inda wasu ke kallonsa a matsayin shawara mai ma’ana da za ta karfafa harkokin masana’antu da jawo jarin cikin gida da na kasashen waje.
Sai dai a daya bangaren kuma, akwai masu sukar wannan mataki, inda suma suka bayyana irin tasu damuwa kan batun.
- NAJERIYA A YAU: Yadda matsalar tsaro ke mana mu tafiye-tafiyen Kirsimeti
- DAGA LARABA: Ko Ziyarar Tawagar Amurka Za Ta Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya?
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba ne kan wadannan takaddama da kuma abun da kowanne gefe ke bayyanawa.
Domin sauke shirin, latsa nan