NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ake Cin Zarafin ‘Yan Najeriya

A wasu lokuta ma, masu rike da madafun iko ne ke cin zarafin, har suna ikirarin cewa babu abin da zai faru

NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ake Cin Zarafin ‘Yan Najeriya

CIN ZARAFIN MATA

Cin zarafi da ake wa daidaikun mutane a Nijeriya a yayin da suke gudanar da ayyukansu na yau da kullum ya zama ruwan dare.

Yawancin mutanen da ake cin zarafisu ba su ma san abin da doka ta tanada game da keta haddin nasu da ake yi ba.

A wasu lokuta ma, masu rike da madafun iko ne ke aikata cin zarafin har suke bugun kirji da cewa babu abin da za a yi musu kan keta maka haddi da suka yi.

Shirin Najeriya A Yau zai yi duba ne kan wannan batu na cin zarafi.

Domin sauke shirin, latsa nan