NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ba Za Mu Sauke Farashin Burodi Ba —’Yan kasuwa

Farashin fulawa da ake amfani da shi wajen sarrafa burodi, gurasa da sauran maƙulashe ya sauka a kasuwa.

NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ba Za Mu Sauke Farashin Burodi Ba —’Yan kasuwa

Burodi

A daidai lokacin da al’umma ke murnar saukar farashin kayayyakin abinci kamar shinkafa da masara da sauran kayan hatsi.

Shi ma farashin fulawa da ake amfani da shi wajen sarrafa burodi, gurasa da sauran maƙulashe ya sauka a kasuwa.

Sai dai duk da saukar farashinta, al’ummar na ci gaba da kokawa kan yadda har yanzu ba su gani a ƙasa ba.

Tun makonni biyu da suka gabata aka sanar da saukar farashin fulawar kamar sauran kayayyakin masarufi.

To amma ba kamar sauran kayan abinci ba, har yanzu ba a ga sauyi a farashin burodi ba.

Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa masu sarrafa burodi suka ƙi sauke farsashinsa duk da karyewar farashin fulawa a kasuwa.

Domin sauke shirin, latsa nan