NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Matan Arewa Karantar Ilimin Kimiyya?
Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai duba ne kan dalilan da suka sa matan Arewacin Najeriya ke tsoron karantar ilimin kimiyya
![NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Matan Arewa Karantar Ilimin Kimiyya? NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Matan Arewa Karantar Ilimin Kimiyya?](https://aminiya.ng/wp-content/uploads/2022/02/Dalibai-a-Fagen-Neman-Ilimi.jpg)
Dakta Zainab Muhammad na daga cikin matan Arewacin Najeriya da ta jajirce tare da ƙudirin cika burinta na karantar kimiyya duk da ƙalubalen da wasu matan yankin ke bayyana cewa suna fuskanta wurin karantar fannin.
Dakta Zainab ba kimiyya kawai ta karanta ba, ta karanci ɗaya daga cikin kimiyyoyin da ake ganin sun fi kowanne wahala wanda a mafi yawan lokuta ba mata kaɗai ba, har da mazan ma na ƙauracewa wannan karatun.
Zainab ƙwararriyar likita ce wacce ta shahara wurin kula da marasa lafiya a asibitoci.
- NAJERIYA A YAU: Shin Har Yanzu Akwai Masu Rufin Asiri A Najeriya?
- DAGA LARABA: Yadda Al’adun Aure A Ƙasar Hausa Suka Koma ‘Event Centre’
Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai duba ne kan dalilan da suka sa matan Arewacin Najeriya ke tsoron karantar ilimin kimiyya.
Domin sauke shirin, latsa nan