NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Wasu Teloli Cika Alƙawari
Shirin Najeriya A Yau, zai yi nazari kan dalilan da suka sa teloli ke kasa cika alƙawari da yadda hakan ke shafar kwastomomi.

A yau, mutane da dama sun fahimci muhimmancin koyon sana’a wajen dogaro da kai, maimakon dogaro da aikin gwamnati ko na kamfani.
Sai dai ana zargin wasu masu sana’ar hannu, musamman teloli, da rashin cika alƙawari.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Mai Karamin Karfi Zai Mallaki Muhalli Da Kudi Kalilan
- NAJERIYA A YAU: Guraben Ayyukan Da Aka Kasa Cikewa A Najeriya
A mafi yawan lokuta, ana samun matsala da su, musamman a lokutan bukukuwa, inda suke kasa kammala ɗinkin kayan da aka ba su ko suka yi alƙawari.
Shirin Najeriya A Yau, zai yi nazari kan dalilan da suka sa teloli ke kasa cika alƙawari da yadda hakan ke shafar kwastomomi.
Domin sauke shirin, latsa nan