Najeriya A Yau: Dalilan kara kudin motar haya lokacin bukukuwa a Najeriya
Wa ke da hannu a irin karin kudin motar haya da ake yi a fadin Najeriya a duk lokacin da bukukuwa suka kusanto?
Domin sauke shirin latsa nan
A duk lokacin da wani biki da zai shafi wasu rukunin al’umma ya taho a Najeriya, wahalarsa ba ta tsayawa a kan masu bikin kadai, hatta ’yan ba ruwanmu sai ta ritsa da su.
A irin wadannan lokuta ’yan Najeriya kan dandana kudarsu wurin biyan motar haya. Amma me ya sa ake haka kuma wa ke da hannu a ciki?