NAJERIYA A YAU: Dalilin ƙulla yarjejeniyar Gwamnatin Kaduna da ’yan ta’adda
Rahotanni sun bayyana cewa Gwamnatin Jihar Kaduna ta ƙulla yarjejeniya da ’yan bindiga. Shin wane alfanu hakan zai haifar?
Kasancewar Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna ɗaya daga cikin yankunan da suka fi fuskantar matsalar tsaro musamman a Arewacin Najeriya.
A kwanan nan rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin jihar ta ƙulla yarjejeniya da ’yan bindiga.
- NAJERIYA A YAU: Dalilan Yawaitar Gobara A Lokacin Hunturu
- DAGA LARABA: Gudunmawar Da ‘Yan Sa Kai Suke Badawa Wajen Yaki Da Matsalar Tsaro
Shirin Najeriya A Yau ya yi nazari ne kan wannan yarjejeniya da kuma abin da hakan ke nufi ga jihar da ma al’ummar yankin.
Domin sauke shirin, latsa nan