NAJERIYA A YAU: Dalilin Da Litar Man Fetur Za Ta Koma N700 A Arewa
Domin sauke shirin kai tsaye, latsa nan A ranar 30 ga watan Mayu da ya gabata ne kamafanin Man Fetur Na Najeriya (NNPCL) ya bayyana cewa sabon farashin man fetur a Arewacin Najeriya ya zama sama da Naira 530 yayin da a Kudancin kasar ya ke tsakanin 470 zuwa 530, biyo bayan tabbatar da cire […]

Man Fetur
Domin sauke shirin kai tsaye, latsa nan
A ranar 30 ga watan Mayu da ya gabata ne kamafanin Man Fetur Na Najeriya (NNPCL) ya bayyana cewa sabon farashin man fetur a Arewacin Najeriya ya zama sama da Naira 530 yayin da a Kudancin kasar ya ke tsakanin 470 zuwa 530, biyo bayan tabbatar da cire tallafin man fetur da sabon shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi a jawabin kama aiki da ya yi ranar 29 ga Mayun 2023.
Mene ne dalilin da ake hasashen litar man fetur zata zama 700 a Arewacin Najeriya, daga 1 ga Yuli na 2023?
- NAJERIYA A YAU: Yadda ’yan Najeriya suka yi Sallah cikin tsadar rayuwa
- DAGA LARABA: Dalilan Lalacewar Al’adun Sallah
Shirin Najeriya A Yau na tafe da bayanan gaskiyar abin da ke faruwa dangane da farashin man fetur din.