NAJERIYA A YAU: Dalilin da ’yan sanda ke kama mutane barkatai

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokacin zai yi duba ne kan sahihancin zargin da ake wa ’yan sanda da kama mutane haka kawai

NAJERIYA A YAU: Dalilin da ’yan sanda ke kama mutane barkatai

‘Yan sanda

Lokacin bukukuwa lokaci ne da ake samun karuwar zirga-zirga da hada-hadar jama’a.

Wannan ne ya sa hukumomin da nauyin samar da tsaro ya rataya a wuyansu suke kara kaimi wajen ganin sun tabbatar da doka da oda.

Sai dai  wasu ’yan Najeriya sukan yi zargin cewa ’yan sanda kan yi amfani da wannan dama don kamen mutane babu gaira babu dalili.

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokacin zai yi duba ne kan sahihancin wannan zargi.

Domin sauke shirin, latsa nan