NAJERIYA A YAU: Dalilin Da Za Mu Kashe Biliyan N2.5 Kan Auren Zawarawa —Gwamnatin Kano

Wasu na ganin jihar na da wasu buƙatun da suka fi auren gatan muhimmanci da ya kamata gwamnatin ta mayar da hankali a kai.

NAJERIYA A YAU: Dalilin Da Za Mu Kashe Biliyan N2.5 Kan Auren Zawarawa —Gwamnatin Kano

Abba Kabir Yusuf

Tun bayan da Gwamnatin Kano ta sanar cewa ta ware Naira biliyan biyu da rabi don aura da ’yan mata da zawarawa a jihar batun ke ta shan suka daga ɓangarori daba-daban.

Wasu na ganin jihar na da wasu buƙatun da suka fi auren gatan muhimmanci da ya kamata gwamnatin ta fi mayar da hankali a kansu.

Shirin Najeriya A Yau na wannan rana ya yi nazari ne kan dalilan da Gwamnatin Kano ta ware Naira biliyan biyu da rabi don aurar da ’yan mata da zawarawa.

Domin sauke shirin, latsa nan