NAJERIYA A YAU: Guraben Ayyukan Da Aka Kasa Cikewa A Najeriya
Sau tari akwai ɗimbin guraben ayyuka da babu masu cike su don babu ƙwararrun da ake buƙata.

Duk da kukan rashin aikin yi da a ko da yaushe ke ci gaba da addabar ‘yan Najeriya, a wasu lokutan ba rashin aikin yi ne matsalar ba, waɗanda za su cike guraben ayyukan ne suka yi ƙaranci a Najeriya.
Alƙaluma na ci gaba da bayyana dubban ‘yan Najeriya ne dai ke fito wa daga manyan makarantun ƙasar a kowace shekara.
A yayin da da yawa ba sa samun aikin yi, sau tari akwai ɗimbin guraben ayyuka da babu masu cike su don babu ƙwararrun da ake buƙata.
- NAJERIYA A YAU: Rashin Aikin Yi Da Hanyoyin Magance Ta A Najeriya
- DAGA LARABA: Asalin Tashe Da Tarihinsa A Ƙasar Hausa?
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokacin zai tattauna ne kan guraben ayyukan da aka kasa cike su da kuma nemo hanyoyi don magance matsalar.
Domin sauke shirin, latsa nan