NAJERIYA A YAU: Hanya daya da farashin man fetur zai iya sauka
Tun bayan cire tallafin man fetur farashin sufuri da kayan masarufi ke ta hauhawa
Abu kamar wasa game da batun karin farashin man fetur, sai ga shi an wayi gari ana siyan shi sama da Naira 600, wanda kuma shi ne kari karo na biyu da aka yi cikin watanni biyu a gwamnati mai ci.
Tun bayan cire tallafin man fetur din a karshen watan Mayu, farashin sufuri da kayan masarufi ya rika hauhawa.
- DAGA LARABA: “Dole Ne Mace Ta Yi wa Mijinta Wanki”
- NAJERIYA A YAU: Wane Ne Zai Zamo Sabon Shugaban Jam’iyyar APC?
Saidai akwai mafita guda daya da yawancin masu ruwa da tsaki suka yi amanna za ta kawo sauƙin man fetur ɗin, in kuwa ba haka ba farashin mai sai abinda hali ya yi.
A cikin Shirin Najeriya a Yau, mun duba hanyoyin da za su iya sa man fetur ya yi sauki ba tare da an sake kara farashi ba.
Domin sauraron shirin ko saukewa kai tsaye, a latsa nan