NAJERIYA A YAU: Yadda harkar Kudi ta intanet ta Sa ’yan Najeriya tafka asara
Rashin karfin intanet na wahalar da ’yan Najeriya wajen yin hada-hadar kudi
Domin saukewa latsa nan.
’Yan Najeriya na kokawa kan rashin tabbas da kuma wahalar da suke sha wajen yin hada-hadar kudi ta intanet.
Yawanci a Najeriya idan mutum zai tura kudi ta intanet yakan kasance cikin fargaba — ko kudin ya ki tafiya, ko kuma ya tafi daga wurinsa, amma ya makale a hanya, ya ki zuwa inda aka tura.
- NAJERIYA A YAU: Manufofin ’Yan Takarar Gwamnan Kano A Zaben 2023
- DAGA LARABA: Dalilin Da Mutane Ke Karya
Shin me ya sa ake yawan samun matsalar harkar kudi ta intanet a Najeriya? Ina mafita?
Shirin Najeriya A Yau ya tattauna da ’yan Najeriya da masana a kan wannan al’amari.