NAJERIYA A YAU: Hukuncin wanke bakin mai Azumi da rana

Shirin Najeriya A Yau ya binciko matsayar manzon Allah akan wanke baki da rana a wurin mai azumi.

NAJERIYA A YAU: Hukuncin wanke bakin mai Azumi da rana

Domin sauke shirin latsa nan

Jama’a da dama na tambayar halacci ko haramcin wanke baki da asuwaki ko burushi da man goge baki da rana a wurin azumi.

Wadansu na ganin bai halatta mai azumi ya wanke bakinsa da rana ba, wadansu kuma na ganin ya halatta.

Shirin Najeriya A Yau ya binciko matsayar manzon Allah (S.A.W) akan wanke baki da rana a wurin mai azumi.