NAJERIYA A YAU: IPOB Na Kassara Tattalin Arzikin Kasuwanci A Dalilin Dokar Zaman Gida
Wasu Al’ummar Kudancin Ƙasar Sam Ba Sa Jin Daɗin Dokar ta IPOB
Aƙalla Shekaru biyu ke nan da ƙungiyar ’yan awaren IPOB ta ƙaƙaba wa mutane zaman gida dole a duk ranakun Litinin a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, a wani mataki na nuna adawa da ci gaba da riƙe jagoransu, Nnamdi Kanu.
Kawo yanzu kasuwancin yankin ya samu koma-baya, sakamakon yadda ake fargabar ziyartar wannan yanki, do da yake su ma wasu mazauna yankin ba su jin dadin tsarin nasu.
- NAJERIYA A YAU: Me Zai Faru Idan Tinubu Bai Miƙa Sunayen Ministoci A Wannan Makon Ba?
- DAGA LARABA: “Dole Ne Mace Ta Yiwa Mijinta Wanki”
A cikin Shirin Najeriya a Yau, mun yi nazari kan ƙalubalen da ’yan kasuwa suke fuskanta saboda dokar zaman gida da IPOB ta kakaba musu.
Domin sauraren cikakken shirin ko saukewa kai-tsaye, a latsa nan