NAJERIYA A YAU: Irin Asarar Da Aka Tafka A Kasuwar Kafintoci Da Ke Kano
Wannan gobara da ba a san musabbabinta ba, ta janyo asarar miliyoyin Naira tare da jefa waɗanda abin ya shafa cikin mawuyacin hali.
Gobara a irin wannan yanayi na iska musamman a kasuwanni da gidaje ba sabon abu ba ne kuma ba abun mamaki ba.
Wasu kafintoci da ke aiki a Kasuwar Lale da ke unguwar Tal’udu a Ƙaramar Hukumar Gwale da ke Jihar Kano sun wayi gari da alhinin gobarar da ta yi sanadiyyar raba su da hanyar abincinsu.
Wannan gobara da ba a san musabbabinta ba, ta janyo asarar miliyoyin Naira tare da jefa waɗanda abin ya shafa cikin mawuyacin hali.
Ko wane irin hasara aka yi a wannan gobara?
- NAJERIYA A YAU: Darasin Da Za a Yi Koyi Dashi Cikin Takaddamar Dangote Da Farukh Ahmed
- DAGA LARABA: Yadda Ragin Farashin Man Fetur Zai Shafi Rayuwar ‘Yan Najeriya
Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan