NAJERIYA A YAU: Kalubalen Da Ke Durƙusar Da Gidajen Rediyo A Arewa
Gidajen rediyo a Arewaci na rufe harkokinsu su ɓace ba tare da an sake jin ɗuriyarsu ba
![NAJERIYA A YAU: Kalubalen Da Ke Durƙusar Da Gidajen Rediyo A Arewa NAJERIYA A YAU: Kalubalen Da Ke Durƙusar Da Gidajen Rediyo A Arewa](https://aminiya.ng/wp-content/uploads/2021/10/radio-mast-tower-telecoms.jpg)
Turakun Kamfanonin Sadarwa
Rediyo na daga cikin kafofin da al’umma da dama suka dogara da su don jin labarai, shirye-shirye da kuma samun nishadi.
Rediyo na taka muhimmiyar rawa wajen wayar wa da al’umma da dama kai musamman duba da yadda aka bayar da shaidar cewa tafi kowace kafa saurin yaɗa bayanai ba a cikin birane ba, har ma da yankunan karkara.
- NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Matan Arewa Karantar Ilimin Kimiyya?
- DAGA LARABA: Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar Hausa
Sai dai a wannan gaɓa ana ganin gidajen rediyo a Arewacin ƙasar nan na samun koma baya, la’akari da yadda a wasu lokutan wasu suke rufe harkokinsu su ɓace ba tare da jin ɗuriyarsu ba.
Domin sauke shirin, latsa nan