NAJERIYA A YAU: ‘Karambanin’ Malamai kan ƙudurorin Harajin Tinubu

Shin karambani ne ya sa malamai tsoma baki a muhawarar ƙudurorin Harajin Tinubu ko neman maslaha ga al’umma?

NAJERIYA A YAU: ‘Karambanin’ Malamai kan ƙudurorin Harajin Tinubu

Kudurorin Dokar Haraji da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike wa Majalisar Dokoki ta Ƙasa suna ci gaba da tayar da kura a Najeriya.

Muhawara a kan batun ta dauki sabon salo ne bayan da wasu malaman addinin Musulunci daga Arewacin Najeriya suka ki amincewa da wasu tanade-tanaden ƙudurorin dokar.

Shin har da su kaza ne a cin danko? Karambani ne ya sa malamai tsoma baki a muhawarar ko neman maslaha ga al’umma? A kan waɗannan batutuwa shirin Najeriya A Yau zai yi nazari.

Domin sauke shirin, latsa nan