NAJERIYA A YAU: Ladan Da Mai Aikin Ƙarfi Yake Samu A Lokacin Azumi

Shirin Najeriya a Yau zai yi duba ne kan irin ladan da masu aikin ƙarfi suke samu yayin da suke azumi.

NAJERIYA A YAU: Ladan Da Mai Aikin Ƙarfi Yake Samu A Lokacin Azumi

Wani mai sana’ar faskare

Watan azumi lokaci ne da akan samu wasu ma’aikatu sun sassauta wa ma’aikata ta hanyar yi musu rangwame kamar rage musu yawan sa’o’in aiki.

Sai dai a lokacin da waɗannan mutane suke samun rangwame, akwai waɗanda suke ayyuka ko sana’o’in da suka dogara da su ciyar da iyalansu.

Sau da dama irin waɗannan mutane sai sun fita sun yi aiki a rana, duk da suna azumi, suke samun abin da za su saka a bakin salati.

Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi duba ne kan irin ladan da masu aikin ƙarfi suke samu yayin da suke azumi.

Domin sauke shirin, latsa nan