Najeriya A Yau: Ma’anar hijabi a idon duniya

Duk da cewa dokokin kasashe sun ba wa dan Adam damar yin addininsa, ana samun ce-ce-ku-ce game da sanya hijabi, wanda umarni ne na addinin Islama.

Najeriya A Yau: Ma’anar hijabi a idon duniya

Raffia Arshad ce alkali mai sa hijabi ta farko a Birtaniya.

Domin sauke shirin latsa nan

 

A yayin da sanya hijabi ya kasance umarnin addinin Islama ga mata domin rufe tsiraici da kare mutuncinsu; dokokin kasashen duniya sun ba wa dan Adam damar yin addininsa ba tare da tsangwama ba.

Sai dai kuma a lokuta da dama ana samun ce-ce-ku-ce game da sanya hijabi ko masu sanyawa.

Shirinmu na yau ya mayar da hankali ne a kan hakikanin ma’anar hijabi.