NAJERIYA A YAU: “Makomar Ɓangaren Ilimi A 2025 Tana Cikin Haɗari”
Shirin Najeriya A Yau zai yi nazari ne a kan alƙiblar da ɓangaren ya fuskanta a shekarar 2025
Ga mai son yin nazari a kan makomar ɓangaren ilimi a Najeriya a 2025, tanade-tanaden kasasfin kuɗi na bana ka iya zama manuniya.
A kasafin kuɗin Gwamnatin Tarayya na 2025 dai, an ware wa ɓangaren ilimi sama da Naira tiriliyon uku.
Wannan ne kuma karo na farko da ɓangaren ya samu irin wannan gata.
Sai dai da alamu hakan bai yi wa malaman makaranta da masu ruwa da tsaki daɗi ba.
- NAJERIYA A YAU: Halin Da Matsalar Tsaro Ya Jefa Arewa A Shekarar 2024
- DAGA LARABA: Abin da ya sa matan wannan zamani ke ƙin auten talaka
Shirin Najeriya A Yau zai yi nazari ne a kan alƙiblar da ɓangaren ya fuskanta a shekarar 2025.
Domin sauke shirin, latsa nan