NAJERIYA A YAU: Makomar Jam’iyyar APC Bayan Zaɓen Ganduje
Ana zargin APC ta kwari Arewa ta Tsakiya da nadin Ganduje, wanda ba daga yankin ta zabo wanda ya maye gurbin Abdullahi Adamu ba
Jam’iyyar APC mai mulki ta tabbatar da tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugabanta na ƙasa. Ko da yake lamarin bai zo da mamaki ba, kasancewar an daɗe ana yaɗa wannan jita-jita, wanda wasu ke ganin shi ya sa babu sunansa a cikin ministoci daga jihar.
Ganduje ya maye gurbin tsohon gwamnan Jihar Nassarawa, Abdullahi Adamu wanda ya sauka bisa raɗin kansa, lamarin da ya sa ake ganin an bar yankin Arewa ta tsakiya babu wani jigo a cikin jamiyyar a matakin kasa.
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Hana ’Yan Najeriya Shiga Zanga-Zangar NLC
- DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Muke Yin Ciko —’Yan Mata
To amma yanzu, mecece makomar jamiyar da inda aka dosa? Shirin Najeriya a Yau ya maida hankali akan hakan
Domin sauraren shirin ko sauke shi kaitsaye, a latsa nan