NAJERIYA A YAU: Matakan da manoman Jihar Taraba suka ɗauka kan ’yan ta’adda
Shirin Najeriya A Yau na wannan rana ya tattauna ne kan irin matakan da al’ummomin yankunan da ’yan ta’adda suka addaba suka ɗauka, don gudanar da ayyukan noma
Wata matsala da ƙasar nan ke ci gaba da fuskanta ita ce ƙarancin abinci sakamakon ’yan ta’adda da ke ɓarnata amfanin gona da hana manoma yin noma, a wasu lokutan ma karɓar kudaden haraji daga manoma suke yi a wasu yankunan.
Hakan ya sa alummomin Karamar hukumar Gassol da Balli dake jihar Taraba daukar wasu matakai don samawa kan su mafita daga ayyukan irin wadannan yan ta’adda.
- NAJERIYA A YAU: Makomar Al’ummar Ƙauyen Tudun Biri Bayan Shekara 1 Da Kai Musu Hari
- DAGA LARABA: Gudunmawar Da ‘Yan Sa Kai Suke Badawa Wajen Yaki Da Matsalar Tsaro
Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai tattauna ne kan irin matakan da al’ummar waɗannan yankuna suka ɗauka don gudanar da ayyukan noma.
Domin sauke shirin, latsa nan