NAJERIYA A YAU: Matakan Da Wasu Al’ummomi Suke Ɗauka Don Guje Wa Ambaliyar Ruwa
Wasu al’ummomi a Najeriya sun fara ɗaukar matakan kauce wa asarar da ambaliyar ruwa ka iya haifar musu idan aka buɗe Madatsar Ruwa ta Lagdo da ke Jamhuriyar Kamaru.

Ambaliya a shatale-talen Baban Gwari da ke Kano
Wasu al’ummomi a Najeriya sun fara ɗaukar matakan kauce wa asarar da ambaliyar ruwa ka iya haifar musu idan aka buɗe Madatsar Ruwa ta Lagdo da ke Jamhuriyar Kamaru.
A kwanan nan ne dai Hukumar da ke Kula da Albarkatun Ruwa ta Najeriya ta ce yankunan da ke gaɓar Kogin Binuwai a jihohi 11 na fuskantar barazanar ambaliyar.
- NAJERIYA A YAU: ‘Mun Yi Zaton Samun Sauki Da Zuwan Matatar Dangote’
- DAGA LARABA: Abin Da Ya Hana Dalibai Da Dama Komawa Makaranta
Shirin Najeriya a Yau zai yi nazari a kan waɗannan matakai da ma hanyoyin magance matsalar gaba ɗaya.
Domin sauke cikakken shirin, latsa nan