NAJERIYA A YAU: Matakan daƙile kisan matafiya a hanyoyin Najeriya
A kwanakin baya ma an kashe wasu matafiya a garin Uromi da ke jihar Edo a hanyar su ta komawa Kano
Matsalar tare fasinjoji da kashe su a hanyoyin Najeriya na ƙara tsananta, musamman a yankunan Arewa.
Misali, a shekarun baya an sha tare matafiya a kashe su a hanyar Abuja zuwa Kano. A kwanakin baya ma an kashe wasu matafiya a garin Uromi da ke jihar Edo a hanyar su ta komawa Kano.
Sai na kwanan nan da ya faru a Jihar Filato inda aka kashe wasu matafiya da ke kan hanyarsu ta zuwa ɗaurin aure.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Tsarin Ilimi Ke Karya Gwiwar ’Yan Najeriya
- DAGA LARABA: Ko Kare Kai Daga Harin ‘Yan Ta’adda Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro?
Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne da nufin gano matakan daƙile afkuwar haka a nan gaba.
Domin sauke shirin, latsa nan