NAJERIYA A YAU: Matakan Samar Da Abinci A Kan Farashi Mai Rahusa A Najeriya

Abin da ya kamata a yi don shawo kan koma bayan da harkar samar da abinci take yi a Najeriya

NAJERIYA A YAU: Matakan Samar Da Abinci A Kan Farashi Mai Rahusa A Najeriya

Manoma

Wadatar da al’umma da abinci abu ne mai matuƙar muhimmanci ga duk ƙasar da ke son zama lafiya ci-gaba.

Sai dai a Najeriya cimma wannan buri na cin karo da ƙalubale, kama daga sauyin yanayi zuwa ambaliyar ruwa da rashin tsaro zuwa ƙarancin zuba jari a ɓangaren noma.

Rahotanni sun nuna cewa adadin abincin da aka samar bai kai yadda ya kamata ba a dalilin waɗannan matsaloli.

Ko me ya kamata a yi don shawo kan wannan mi’ara koma baya da harkar samar da abinci take yi a Najeriya?

Wannan shi ne batun da aka duba yayain Taron Muhawara na Shekara-Shekara na Daily Trust na bana, kuma a kansa shirin Najeriya a Yau za yi tsokaci.

Domin sauke shirin, latsa nan