Najeriya A Yau: Matasan Arewa: Da noma gara zaman jiran tsammani
Dalilin da matasa ke zaman jiran aikin ofis alhali wadanda suka shiga harkar noma sun yi gaba sun bar su
Domin sauke shirin latsa nan
Allah Ya yi wa matasan da ba su da ba aikin yi a Najeriya yawa sosai, duk kuwa da irin baiwar da Allah Ya yi wa kasar na filin noma da gulaben da za a iya amfani da su wurin noma rani da damana.
Shirin Najeriya A Yau ya gano dalilan wadannan matasa da ke zaman jiran aikin ofis da kuma wadanda suke noman da yadda suka fara.