NAJERIYA A YAU: Matsayar Doka Kan Taron Da Jam’iyyar PDP Ta Gudanar
Duk da waɗannan hukunce-hukunce, jam’iyyar ta gudanar da taron inda ta zaɓi shugabannin da za su ci gaba da jan ragamar al’amuranta
Matsayar doka ta zama babbar abin tattaunawa a Najeriya bayan da Jam’iyyar PDP ta gudanar da taronta na ƙasa duk da mabambanta hukunce-hukunce daga kotuna biyu.
Umarnin kotu guda yana goyon bayan taron, ɗayan kuwa ya haramta shi gaba ɗaya. Wadannan hukunce-hukunce ba baiwa jam’iyyar damar yi ko haramta musu taron kaɗai suka yi ba, har da baiwa hukumar zaɓe ta ƙasa umarnin saka ido ko haramta musu wannan dama na yayin taron.
Duk da waɗannan hukunce-hukunce, jam’iyyar ta gudanar da taron inda ta zaɓi shugabannin da za su ci gaba da jan ragamar al’amuranta da kuma ɗaukar wasu ƙwararan matakai.
- NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Manoman Najeriya Noman Rani
- DAGA LARABA: Tasirin Da Tura Jami’an ‘Yan Sanda Kare Manyan Mutane Zai Haifar Ga Tsaron Al’umma
Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan