NAJERIYA A YAU: Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati Ba

Abun da dokar kasa ta ayyana kan umarnin da gwamna Muhammad Umar Bago ya bada kan hawan malamai mumbari.

NAJERIYA A YAU: Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati Ba

Gwamnan Jihar Neja, Umaru Bago

Matakin hana malaman da ba su da rajista hawa mumbari domin yin wa’azi a Neja yana ci gaba da yamutsa hazo a ciki da wajen jihar.

Yayin da wasu suke ganin matakin bai dace ba, wasu kuwa gani suke faduwa ce ta zo daidai da zama, wato matakin ya zo a daidai lokacin da ake buƙata.

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kan tanadin dokar ƙasa game da wannan batu.

Domin sauke shirin, latsa nan