NAJERIYA A YAU: Me Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Su Ga Ragi A Farashin Man Fetur Ba?
Sai dai har yanzu ba a ga ragin a gidajen mai ba

Man fetur
Fiye da wata guda ke nan bayan da Matatar mai ta Ɗangote ta sanar da rage farashin man fetur daga naira 890 zuwa naira 825 kowace lita.
Bayan wannan ragi ne dai shi ma Kamafanin Mai na Kasa (NNPCL) ya sanar da rage nasa farashin. Sai dai har yanzu ba a ga ragin a gidajen mai ba.
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa Ba Mu Bayar da ‘Ramadan Basket’ Ba
- DAGA LARABA: Yadda Zawarawa Suke Ɗanɗana Kuɗa A Watan Ramadana
Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan wannan lamari.
Domin sauke shirin, latsa nan