NAJERIYA A YAU: Me ya sa A Ke Naɗa Yan Arewa Ministocin Tsaro?
Yawancin ministocin da ake naɗa wa a fannin tsaro daga yankin Arewa suka fito

Babban Minista da ƙaramin Ministan tsaron gwamnatin Tinubu, Badaru da Matawalle
Ƙididdiga ta nuna cewa yawancin ministocin da ake naɗawa su jagoranci fannin tsaron Najeriya a mulkin dimokraɗiyya suna fitowa ne daga yankin Arewa.
Ƙalubalen tsaro ya fi ƙamari a wannan yanki, abin da ya sa wasu ke ganin hakan wani salo ne da zai sa su maida hankali wajen magance damuwar yankin.
- NAJERIYA A YAU: Yadda hauhawar farashi ke hana ’yan Najeriya cin abinci
- DAGA LARABA: Mece Ce Ribar Kai Gwamnati Ƙara
A cikin shirin Najeriya A Yau, mun duba tasirin da nadin ’yan Arewa a matsayin ministocin tsaron gwamnatin Tinubu zai yi wajen magance matsalolin tsaron yankin.
Domin sauraren shirin, latsa nan