NAJERIYA A YAU: Nasarori da ƙalubalen da Bankin Musulunci ke fuskanta a Najeriya

Yadda bankin Musulunci ya samo asali, ci-gabansa da kuma irin ƙalubalen da yake fuskanta a Najeriya.

NAJERIYA A YAU: Nasarori da ƙalubalen da Bankin Musulunci ke fuskanta a Najeriya

A Jamhuriya ta Huɗu a Najeriya, wadda ta fara a shekarar 1999, an samu sauye-sauye masu yawa a ɓangaren tattalin arziki da harkokin kuɗi, ciki har da tasowar bankunan Musulunci.

Wannan tsari na banki ya samo asali ne daga buƙatar samar da hanyoyin mu’amala da kuɗi da suka dace da koyarwar addinin Musulunci, wato hanyoyin da ba su ƙunshi riba, da zamba, ko rashin tabbas ba.

A farkon lokaci, ra’ayin kafa bankunan Musulunci ya fuskanci muhawara da adawa daga wasu ɓangarori na al’umma, musamman saboda fahimtar da ake yi cewa tsarin na da alaƙa da addini.

Sai dai daga bisani, gwamnati da hukumomin kula da harkokin banki, musamman Babban Bankin Najeriya (CBN), sun samar da dokoki da ƙa’idoji da suka bai wa bankunan Musulunci damar aiki a matsayin bankunan da basa cin riba.

Shirin Najeriya  A Yau na wannan lokaci zai yi duba ne a kan tasowar bankunan Musulunci da ƙalubalen da suke fuskanta.

Domin sauke shirin, latsa nan