NAJERIYA A YAU: Rashin Aikin Yi Da Hanyoyin Magance Su A Najeriya.
Me ke ƙara kawo ƙaruwar rashin aikin yi kuma ta yaya za a magance matsalar a Najeriya?
Rashin aikin yi na daga cikin manyan ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta a wannan lokaci, musamman la’akari da yadda ake ƙara samun matasa masu jini a jika amma babu aikin yi.
Rahoton Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa ya nuna an samu ƙaruwar rashin aikin yi da kaso 5.3% a farkon wannan shekarar a Najeriya.
Kazalika binciken yana nuni da cewa waɗanda ba su yi karatu mai zurfi ba sun fi waɗanda suka yi samun aikin yi.
Me ke kawo ƙaruwar rashin aikin yi a Najeriya kuma ta
waɗanne hanyoyi za a wajen magance matsalar?
Waɗannan da ma wasu tambayoyi na cikin batutuwan da shirin Najeriya A Yau zai yi duba a kai.