NAJERIYA A YAU: Rashin aikin yi da hanyoyin magance su a Najeriya
Wadanne dalilai ne ke kara kawo rashin aikin yi a Najeriya kuma wadanne hanyoyi za a bi wajen magance matsalar?
Rashin aikin yi na daga cikin manyan kalubalen da Najeriya ke fuskanta a wannan lokaci, musamman la’akari da yanda ake ci gaba da samun matasa masu karfi a jika amma babu aikin yi.
Rahoton Hukumar Kididdiga ta Kasa ya nuna cewa rashin aikin yi ya karu a Najeriya da kaso 5.3 a farkon wannan shekarar. Kazalika binciken ya bayyana cewa wadanda ba su yi karatu mai zurfi ba sun fi wadanda suka yi samun aikin yi.
- NAJERIYA A YAU: Ko Kawo Dakarun Amurka Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya?
- DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa PDP Ta Ki Sayarwa Sule Lamido Fom Din Takarar Shugaban Jam’iyya
Wadanne dalilai ne ke kara kawo rashin aikin yi a Najeriya kuma wadanne hanyoyi za a bi wajen magance matsalar?
Wadannan da ma wasu tambayoyi na cikin batutuwan da shirin Najeriya A Yau zai yi duba a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan