NAJERIYA A YAU: Yadda Rashin Wutar Lantarki Ya Jefa ’Yan Najeriya Cikin Kunci

Tsananin zafi da tsadar mai sun sa ’yan Najeriya kokawa kan karuwar matsalar wutar lantarki

NAJERIYA A YAU: Yadda Rashin Wutar Lantarki Ya Jefa ’Yan Najeriya Cikin Kunci

Domin sauke shirin latsa nan

A yayin da kusan kowane bangare na rayuka ke kara dogaro da amfani da wutar lantarki, samuwar watar sai kara wuya take a Najeriya, inda a halin yanzu bukatar wutar ke karuwa saboda matsanancin zafi da tsadar man fetur.

Shirin Najeriya  A Yau na dauke da yadda ’yan kasar ke rayuwa a cikin duhu, rashin tabbacin samun wutar da kuma musabbabin matsalatar, wadda ta sa cibiyoyin kiwon lafiya, masana’antu, da sauran bangarori kokawa.