NAJERIYA A YAU: Rawar Da Fassara Ke Takawa Wajen Haɓaka Harshen Hausa
Tattaunawa kan irin gudunmawar da fassara ke bayarwa wajen haɓaka harshen Hausa.

Yau ce Ranar Fassara ta Duniya wadda Majalisar Dinkin Duniya ta ware don jinjina ga ayyukan ƙwarrarrun da suke haɗa al’ummomi waje ɗaya, da ƙarfafa zaman lafiya da tsaro a duniya ta hanyar juya bayanai daga wani harshe zuwa wani.
Albarkacin wannan rana, shirin Najeriya A Yau zai tattauna ne kan irin gudunmawar da fassara ke bayarwa wajen haɓaka harshen Hausa.