NAJERIYA A YAU: Cushe-cushen Da Ake Zargin An Yi A Sabbin Dokokin Haraji

A ɗaya ɓangaren kuma, Fadar Shugaban Ƙasa ta yi nuni da cewa abin da aka yi gyara ne na fasaha da tsari, ba sauya ma’anar doka ba.

NAJERIYA A YAU: Cushe-cushen Da Ake Zargin An Yi A Sabbin Dokokin Haraji

Hukumar Tara Kudin Shiga ta Tarayya (FIRS) ce ke karbar haraji a madadin Gwamnatin Tarayya

Takaddama mai zafi ta dabaibaye sabbin dokokin haraji da Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta amince da su, bayan zarge-zargen cewa an yi sauye-sauye a cikin dokokin ta bayan fage, bayan an kammala dukkan matakan amincewa da su a majalisa.

Batun da ya taso ya jawo cece-kuce daga ’yan majalisa, jam’iyyun adawa da ƙungiyoyin fararen hula, inda suke tambayar sahihancin abin da aka miƙa wa Fadar Shugaban Kasa domin aiwatarwa.

Masu suka na cewa sauye-sauyen da ake zargin an yi ba tare da amincewar majalisa ba na iya lalata tsarin dimokuraɗiyya, tare da haifar da rashin gaskiya da riƙon amana a tsarin dokoki.

A ɗaya bangaren kuma, Fadar Shugaban Ƙasa ta yi nuni da cewa abin da aka yi gyara ne na fasaha da tsari, ba sauya ma’anar doka ba.

Ko waɗanne irin sauye-sauye aka yi wa sabuwar dokar harajin?

Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.

Domin sauke shirin, latsa nan