NAJERIYA A YAU: Shin Har Yanzu Akwai Masu Rufin Asiri A Najeriya?

Shin a iya cewa har yanzu akwai masu matsakaicin ƙarfin aljihu a Najeriya?

NAJERIYA A YAU: Shin Har Yanzu Akwai Masu Rufin Asiri A Najeriya?

Yadda ake hada-hada a wata kasuwa a Najeriya.

Akan karkasa mutane gida-gida a bisa mizanin tattalin arziki, musamman a tsarin jari-hujja, inda ke da mawadata da kuma matalauta.

A tsakanin al’umma kuma akwai ajin mutane masu matsakaicin samu waɗanda ake kira “Middle Class”.

Akan sanya mutane a wannan aji ne galibi bisa la’akari da aiki ko sana’ar da suke yi, da kuɗin da suke samu, da matakin ilimin da suka kai, da ma matsayinsu a tsakanin al’umma.

Sai dai a baya-bayan nan irin wadannan muntane sun bi sahun matalauta wajen korafi game da yadda suke dandana kudarsu saboda tsadar rayuwa.

Shin a iya cewa har yanzu akwai wannan aji na mutane a Najeriya ke nan?

Wannan ne batun da shirin Najeriya  a Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.

Domin sauke shirin, latsa nan