NAJERIYA A YAU: Shin da gaske NLC za ta iya shiga yajin aiki kuwa?

Wasu na ganin kamar ƙungiyoyin ƙwadago sun zama macijin roba

NAJERIYA A YAU: Shin da gaske NLC za ta iya shiga yajin aiki kuwa?

ƙungiyoyin ƙwadago

A lokuta da dama idan gwamnati ta ɓullo da wani tsarin da ya ci karo da muradun talakawa, ana sa ran ƙungiyar ƙwadago ta shige gaba wajen adawa da shi har sai an sauya matsaya.

Daya daga cikin hanyoyin da suke bi ita ce yajin aiki. Sai dai irin wannan gargaɗi na yajin aiki da zanga-zanga da kungiyoyin ƙwadago ke yi a Najeriya, wasu na ganin barazana ce kawai amma ba sa iya aiwatar da komai, domin suna ganin kamar sun zama macijin roba. Ko da yake ƙungiyoyin ƙwadagon na cewa ba su samun goyon baya daga talakawan.

Shirin Najeriya A Yau, ya yi nazari a kan ko ƙungiyoyin ƙwadago za su iya fafutuka don talaka ba wai aljihunsu ba.

Domin sauraren cikakken shirin ko saukewa kai tsaye, a latsa nan

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta