NAJERIYA A YAU: Shin Ya Kamata A Sanya Sarakuna A Kundin Tsarin Mulkin Ƙasa?

Sarakunan gargajiya na taka mahimmiyar rawa wajen gudanar da mulki da cigaban al’umma, saidai za a iya cewa babu wata saɗara da ta fayyace aikin su ƙarara a kundin tsarin mulki, lamarin da sarakunan ke cewa da yawa daga cikin ‘yan siyasa, da zarar sun ci zaɓe sukan manta da su. Wasu na ganin lokaci […]

NAJERIYA A YAU: Shin Ya Kamata A Sanya Sarakuna A Kundin Tsarin Mulkin Ƙasa?

Sarakunan Gargajiya

Sarakunan gargajiya na taka mahimmiyar rawa wajen gudanar da mulki da cigaban al’umma, saidai za a iya cewa babu wata saɗara da ta fayyace aikin su ƙarara a kundin tsarin mulki, lamarin da sarakunan ke cewa da yawa daga cikin ‘yan siyasa, da zarar sun ci zaɓe sukan manta da su.

Wasu na ganin lokaci ya yi da ya kamata su kasance a hukumance cikin kundin, duk da yake wasu na ganin hakan zai iya rage ƙimar da suke da shi idan suka tsunduma harkokin gwamnati da siyasa.

A cikin Shirin Najeriya a Yau, mun yi nazari akan sama wa sarakunan gargajiyar matsayi a kundin tsarin mulkin ƙasa, ganin irin rawar da suke takawa a cikin al’umma.

Domin sauraren shirin ko saukewa kaitsaye, a latsa nan