NAJERIYA A YAU: Tanadin Dokar Kasa Kan Kirkirar Gwamnatin Bibiya A Kano
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan halascin kafa gwamnatin bibiya a Jihar Kano.

(Hoto: Shutterstock).
Tun bayan sanarwar shirin kafa gwamnatin bibiya ko kuma ‘shadow government’ a turance da wata kungiya ƙarƙashin Jam’iyyar APC a Jihar Kano tace za ta yi ne ne dai al’umma da dama ke ta jefa ayar tambaya kan halascinta.
Kungiyar dai ta bayyana cewa za ta kafa wannan gwamnati ne don bibiyan ayyukan gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf don tabbatar da ana abin da ya kamata.
Sai dai wannan sanarwa na ci gaba da yamutsa hazo inda wasu ke kallon halascin wannan gwamnati.
- NAJERIYA A YAU: Ci-gaban Da Hukumomin Raya Shiyyoyi Za Su Samar
- DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ke Haɗa Buga-Buga Da Aikin Albashi
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan halascin kafa gwamnatin bibiya a Jihar Kano.
Domin sauke shirin, latsa nan