NAJERIYA A YAU: Tasirin Siyasar Matasa Tun Bayan Dawowar Jamhuriya Ta Hudu
Yadda Siyasar matasa Take tun bayan dawowar dimokradiyya a jamhuriya ta hudu.
Shekaru kafin a sanya hannu kan Dokar Not Too Young To Run, siyasar matasa a Najeriya na fuskantar ƙalubale masu tarin yawa.
Duk da cewa matasa su ne mafi rinjaye a yawan al’umma da kuma masu katin zaɓe, an dade ana kallon su a matsayin masu ɗaukar tutoci, da yaɗa saƙonni ko kuma masu tayar da tarzoma a lokacin zaɓe, ba tare da ba su cikakkiyar dama ta tsayawa takara ko shiga manyan matakan yanke shawara ba.
Sai dai a shekarar 2018, bayan sa hannu kan dokar bai wa matasa dama a siyasar Najeriya, an samu sabon salo da fata a fagen siyasa.
Dokar ta rage shekarun tsayawa takara a muƙaman siyasa daban-daban, tare da buɗe ƙofa ga matasa masu ƙwazo, da ilimi da kishin ƙasa su shiga fafutukar jagoranci kai tsaye.’
- NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Mallakar Gida Ga Mai Ƙaramin Ƙarfi
- DAGA LARABA: Shin Ko Dawowar Dimokradiyya Ta Samar Da Kyakkyawan Fata Ga ‘Yan Najeriya?
Wannan mataki ya ƙarfafa gwiwar matasa da dama su fara ganin siyasa a matsayin fagen da za su iya kawo sauyi, ba wai kawai a matsayin masu goyon baya ba.
A ci gaba da kawo muku shirye gabanin muhawarar Daily Trust, shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi duba ne kan yadda siyasar matasa ta kasance a Jamhuriya ta Huɗu tun bayan ayyana wannan doka.