NAJERIYA A YAU: Wane Mataki Za A Ɗauka Kan Cin Zarafi Da Kisan ’Yan Jarida?
Jami’an tsaro na yawan yi wa ’yan jarida kisan gilla ko cin zarafinsu, da nufin hana su daukar rahoto

Ana yawan kai ruwa rana tsakanin ‘yan jarida da jami’an tsaro
A duk lokacin da wani muhimmin abu ya taso, ’yan jarida na kan gaba wajen fadi-tashin kawo wa jama’a rahotanni tare da fayyace musu ainihin abin da ya faru.
Sai dai a lokuta da dama wasu jami’an tsaro kan hana ’yan jarida shiga wasu wurare domin samo rahoto, inda a garin hakan suka yi wa ci zarafin ’yan jaridar, ko ma su kashe su, musamman idan abun ya shafi manyan jami’an gwamnati.
- NAJERIYA A YAU: Me Zai Faru Bayan Hukuncin Kotu Kan Zaɓen Kano?
- DAGA LARABA: Matakan Nasara Wajen Neman Aure A Soshiyal Midiya
Shirin Najeriya A Yau ya duba matakan da ya kamata a ɗauka game da masu yi wa ’yan jarida kisan gialla ko cin zarafinsu.
Domin sauraren shirin, latsa nan